Rahotanni Daga Kasar Indiya.
Kimanin mutane 100 zuwa 150 ne ake fargabar ambaliyar ruwa ta yi Awon gaba dasu a can Gundumar Chamoli dake Jihar Uttarakhand ta kasar Indiya, A cewar kamfanin dillancin labarai na ANI.
Kamfanin Dillancin Labaran ya rawaito cewa tuni hukumomin kasar suka aike da kwararrun masu aikin ceto domin cetar mutane da Ambaliyar ta rutsa dasu.
Ambaliyar ta haifar da karyewar babbar gadar dake a yankin tare da lallata wasu Turakun wutar lantarki wanda a halin yanzu ake kan gyarawa.