Sunday, June 7
Shadow

Ana gudanar da bincike akan wani mutum da ake zargin ya kamu da cutar Coronavirus a jihar yobe inda ake dakon sakamakon gwajin nashi daga abuja

Zargin cutar Coronavirus yasa an aike da jini wani mutum mai kimanin shekaru 30 zuwa Abuja domin bincika ko yana dauke da cutar Covid-19 inda kuma ake sa ran sakamakon zai fito nan da cikin awanni 48 masu zuwa, Kwamishinan Lafiya Dr. Mohammed Lawan Gana ne ya bayyana haka.

Kwamishinan, wanda ya bayyana lamarin ga manema labarai a maraice Jumma’a,

Amma ya ce ba za a iya bayyana mara lafiyan a matsayin wanda ya kamu da cutar COVID 19 ba har sai abun da sakamakon ya nuna daga Abuja.

A cewar Kwamishinan, mara lafiyar direban mota ne mai shekara 30, wanda ya zo daga Legas zuwa Potiskum amma bai yi cuɗanya da danginsa ko makwabtan sa ba.

Ya ce,: “An gabatar da diraban motar a matsayin mara lafiya a ranar 2 ga Afrilu 2020 tare da alamun tari, zazzabi da wahalar numfashi na kwanaki shida.

Sai dai ya bayyana suna jiran sakamako daga abuja domin tabbatarwa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *