Eh, Ana haihuwa a wata takwas amma mafi yawanci dan sai an bashi kulawa ta musamman.
Saidai kada ki tayar da hankalinki mafi yawanci duk wanda aka haifa a wata 8 sukan rayu kuma su yi rayuwa irin ta kowa.
Kai har wanda ma aka haifa a wata bakwai sukan rayu su kuma yi rayuwa irin ta sauran mutane bayan an basu kulawa ta musamman bayan haihuwarsu.
Dan haka idan kika haihu a wata 8 kada hankalinki ya tashi, kiwa abinda kika haifa fatan Alheri.
Dalilin da yasa ake haihuwa a wata 8 ko wata 7 wanda ake cewa bakwaini:
Idan kofar mahaifarki bata da kwari, ya kai cewa bata iya rike dan da zaki haifa, hakan na iya faruwa, za ta bude ki haihu a wata na 7 ko 8.
Idan ya zamana kin taba haihuwa a wata na 7 ko 8, hakan zai iya sake faruwa.
Idan ‘yan Biyune suma ana iya haihuwarsu lokaci bai yi ba.
Idan mahaifiyar na da wata matsalar rashin lafiya data sa sai an fitar da dan daga jikinta.
Idan ya zamana mahaifa na da matsala.
Idan riwan dake baiwa dan cikinki kariya ya fashe.
Idan mahaifiyar na da ciwon sugar ko waninsa.