An kaddamar da shirin tallafawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour party, Peter Obi da tallafin Naira biliyan 100.
Za’a samu kudadenne daga hannun ‘yan Najariya da zasu bayar da tallafin taro sisi daga aljihunansu kamar dai yanda akawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari Buhari a shekarar 2015.
Me ikirarin fafutuka, A’isha Yesufu ce zata jagoranci hada wadannan kudade.
Da take bayani kan dalilin tara kudaden, A’isha Yesufu ta bayyana cewa, dan siyasa me yakin neman zabe na bukatar kudi.
Tace kuma Peter Obi baya kan mulki ballantana ya samu kudaden da zai yi amfani dasu wajan yakin neman zabe.
Tace dan haka ‘yan Najariya zasu bashi nasu tallafin.