Tsohon wakilin Robert Lewandowski, Cezary Kucharski ya bayyana cewa dan wasan mai shekaru 33 na tsoron taka leda a kasar Ingila.
Inda yace Lewamdowski baya jin cewa zai bunkasa sosai a kasar Ingila kamar yayi a kasar Jamus, kuma lewandowski baya son ruwan sama sosai tun yarintarsa kuma gashi anayi a Ingila.
Ya bayyana hakan ne bayan da wasu rahotanni ke bayyaba cewa yaki komawa Chelsea saboda yana so yaje Barcelona, kuma gashi Chelsea a neman shi ya maye mata gurbin Lukaku wanda zata sayarwa Inter.