fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Ana sakaci da tsaro a iyakokinmu>>Gwamna Ganduje

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ko kadan bai gamsu da yadda ake tsare iyakokin jihar da ya bayar da umarni ba.

 

 

Ganduje, ya shaida wa BBC cewa direbobin motoci musamman na haya yanzu sun gano wasu hanyoyi da suke bi su shiga cikin jihar ba tare da sanin jami’an tsaro ba.

 

 

Ya ce ” A gaskiya ba mu gamsu da yadda ake tsare iyakokinmu ba musamman na kasa don ana barin motoci ba tare da sun dauko komai ba su shiga cikin jihar”.

 

 

Gwamna Ganduje ya ce a lokuta da dama direbobi kan ajiye fasinja kafin a iso wajen da jami’an tsaro suke, sai fasinjan su tafi a kafa ko a dauke su a babur sai su hadu a can gaba bayan jami’an tsaro sun duba motar sun ga ba kowa.

 

 

Ya ce ” Wannan dabarace don haka ba zamu yarda da irin wannan abun ba”.

 

Gwamnan ya ce shi da kansa ya kama wasu mutane da suka so shiga jihar wadanda suka zo daga garin Madalla da ke jihar Neja.

 

 

Ganduje ya ce, muddin ana barin irin wadannan mutanen da suka fito daga wasu garuruwa musamman wuraren da aka samu bullar coronavirus suna shiga cikin jihar, to za a iya kai musu cutar.

 

 

Ya ce ” Sam ba zamu lamunci a kai mana cutar da bamu da ita ba, tun da har yanzu ba a samu bullarta a jihar mu ba”.

Karanta wannan  Hotuna: Kungiyar kiwon lafiya ta kaiwa shugaba Buhari ziyara a fadarsa

 

 

Gwamnan dai na wannan jawabin ne bayan korafin da wasu mutane a jihar suka yi cewa akwai sakaci a game da yadda ake tsare iyakokin jihar musamman na kasa.

 

 

Masu korafin sun ce har yanzu ana barin mutane daga wasu jihohi suna shiga cikin Kano bayan kuma tuni aka rufe dukkan iyakokin shiga jihar don gujewa bullar coronavirus cikin Kanon.

 

 

A daren 27 ga watan Maris, 2020, ne gwamnatin jihar ta Kano ta bayar da umarnin rufe dukkan iyakokinta da nufin hana shige da fice zuwa sauran jihohin kasar ta yadda za a dakile yiwuwar baza cutar coronavirus.

 

 

Kawo yanzu dai ba a samu bullar cutar a jihar Kano ba, sai dai gwamnatin ta ce matakin riga-kafi ne kuma a cewarta ya shafi “wadanda su ma suke son shiga Kano ta hanyar jirgin saman Malam Aminu Kano, don haka ko matafiyi ya sauka a filin jirgin na Kano, to ba zai samu shiga cikin kwaryar birnin ba.”

 

 

Kazalika matakin zai taimaka wajen takaita shigar baki ‘yan kasuwa zuwa jihar Kano a yanzu, a dai-dai lokacin da ake daukar matakan rage cunkoso don kare mutane daga annobar coronavirus.

 

 

Yanzu haka Najeriya na da jumullar mutanen da suka kamu da cutar ta coronavirus 131 a fadin kasar, inda biyu daga cikinsu suka mutu, sannan takwas kuma sun warke.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.