fbpx
Friday, March 31
Shadow

Ana samun ƙaruwar fyade da Boko Haram ke yi wa yara mata da manya a Najeriya>>Amnesty

Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Amnesty ta ce ana samun ƙaruwar aikata laifukan fyaɗe da Boko Haram ke yi wa yara mata da manya, kuma hakan abin damuwa ne sosai.

Amnesty ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakan gaggawa domin shawo kan matsalar.

Ƙungiyar a wata sanarwa da ta fitar a yau Laraba, ta ce “mayakan Boko Haram sun addabi mata da ƙananan yara suna cin zarafinsu da lalata”.

Sabon binciken da Amnesty ta wallafa ya ce laifukan da mayaƙan ke yi ba shi da maraba da aikata laifukan yaƙi a arewa maso gabashin Najeriya.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *