fbpx
Monday, March 1
Shadow

Ana samun Rahotanni Masu karo da juna kan sakin daliban makarantar Kagara

Rahotanni daga jihar Naija sun bayyana cewa an saki daliban Makarantar Kagara da Malamansu da aka sace.

 

A ranar Lahadi, Jami’an gwamnatin jihar Naija sun bayyana cewa an saki daliban suna kan hanyarsu ta komawa Minna inda gwamnan jihar da mukarrabansa suna can suna jiran zuwansu.

 

Hakanan wata Majiyar tsaro ta bayyanawa Punchng cewa daliban na Hanyar Birnin Gwari dan komawa gida.

 

Saidai da yammacin jiya, Lahadin, Misalin Karfe 11PM na dare gwamnan jihar Naija, Abubakar Bello da yake magana da iyayen daliban yace har yanzu suna tsare a hannun wanda suka yi garkuwa dasu amma suna kokarin ganin sun kubutar dasu.

 

Abin jira dai a gani shine yaushe aiban zasu samu ‘yanci.

 

“We still have the students of Kagara in the hands of the bandits and everything is being done to secure their release soonest,” the governor said.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *