fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Ana tuhumar tsohon gwamnan Zamfara, Yariman Bakura bisa yiwa wani dan kasuwa Barazanar rayuwa

An gurfanar da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani Yariman Bakura a gaban wani kwamitin Sulhu ranar 10 ga watan Fabrairu bayan da yayiwa Wani dan kasuwar jihar Katsina, Alhaji Musa Wafa Barazanar Rayuwa.

 

Ana tuhumar tsohon gwamnan da sa ‘Yansanda su kamo dan kasuwar da azabtar dashi saboda bashin Naira Miliyan 23.

 

A yayin zaman tattaunawar an nemi Sanata Yerima da dan kasuwar idan zai yiyu su je su daidaita kansu kuma sun amince da hakan.

Dan kasuwar ya bayyana cewa Sanata Yerima na binshi bashin Naira Miliyan 23 hakanan shima yana bin sanatan Bashin Miliyan 5 na Masara Tirela 3 da ya kai masa gidan Gona.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *