fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Ana turka-turka tsakanin jam’iyyu da INEC a Najeriya

A Najeriya, an shiga turka-turka tsakanin jam’iyyun siyasar kasar da hukumar zabe game da bukatar jam’iyyun ta neman karin wa’adi kan zaben fitar da gwani da gabatar da ‘yan takara.

Hukumar zaben, INEC dai ta ce tana nan a kan matsayinta na wa’adin ranar uku ga watan Yuni don jam’iyyu su kammala zabukan fitar da gwani.

Sai dai, jam’iyyun kasar ta bakin majalisar tuntuba tsakanin jam’iyyu sun ce wa’adin ya takura musu, duk da yake bukatarsu ba ta saba wa tsarin mulki ba.

A hirarsu da BBC Shugaban majalisar jam’iyyun, Injiniya Yabagi Sani ya bayyana dalilinsu na neman hukumar zaben ta kara musu wa’adi.

Ya ce tun da ita kanta dokar sabuwa ce, ya kamata INEC, ta duba bukatar tasu, domin suna gudun kada su yi abu cikin gaggawa kuma a zo a samu wata jayayya ta shari’a a kotu.

Ya kara bayani da cewa, ”To shi ne ya sa muka kira ita hukumar zabe cewa don Allah su sake dubawa su ga yanda za a yi a ba jam’iyyu, a ba mu lokaci har zuwa August ba June ba, a kara mana wata biyu tun da bai shiga abin da constituition ta ce ba, bai taba wannan wata shida da kundin mulki ya tanada ba.”

To amma kuma Injiniya yabagi ya ce, da suka gabatar wa da shugaban hukumar zaben wannan bukata, ya shaida musu cewa idan har suka sauya, abin zai iya haifar musu da matsaloli.

Amma ya ce shugaban ya yi musu alakawrin cewa za su je su duba bukatar.

”Su dai nasu a matsayinsu na hukuma su ga cewa an yi zaben a bisa doka, amma zaben ainahin zaben, ai jam’iyyu ne za su yi ba su za su yi ba.” In ji shi.

To, sai dai a karin bayanin da ta yi wa BBC, mai magana da yawun hukumar zaben ta Najeriya, Hajiya Zainab Aminu, ta jaddada cewa kara wa’adin zai iya rikita jadawalin zaben da hukumar ta riga ta fitar, saboda hak INEC na kan bakanta.

Ta ce, sai biyu a cikin sati biyu da ya gabata hukumar ta zabe ta yi wa jam’iyyu tuni a kan muhimmancin kiyayewa da jadawalin zabe na 2022 musamman ma batun fitar da ‘yan takara, dokar da ta riga ta fitar tun ranar 26 ga watan Fabrairu na 2022.

Jami’ar ta INEC, ta yi nuni da cewa har kullum hukumarsu tana aiki ne da dokokin zabe na 2022:

” Wanda kuma idan aka duba sashe na 29, sakin layi na daya, doka ta tanadar da dukkan jam’iyyun siyasa su aike da sunayen ‘yn takarkarinsu da suka tsaida bayan gudanar da abuka na cikin gida kafin kwanaki 180 g ranar babban zabe.” in ji ta.

A karshe mai magana da yawun INEC din ta ce, hukumar zaben tana nan a kan bakanta, kuma ta jaddada bukatar ganin jam’iyyun na najeriya sun ci gaba da gudanar da shirye-shiryensu, tare da gudanar da zaben fitar da ‘yan takararsu kamar yadda aka tsara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.