Matsanancin karancin Man fetur ya shiga jihar Zamfara inda hakan yasa rayuwa ta yi tsada.
Wasu ‘yan kasuwa sun bayyanawa majiyarmu cewa, dalilin haka mutane basa zuwa sayen kaya sosai kamar a baya.
Hakanan wasu mutane a jihar dole sun koma tafiyar kafa saboda abin hawa yayi tsada.
Wani da aka zanta dashi yace shi da iyalansa ba zasu yi zabe a shekarar 2023 ba saboda basu ga ribar dimokradiyya ba.
Yace ya kammala aiki na shekaru 35 a jihar inda ake biyansa albashin Naira N7,500 yace ta yaya kasarnan zata gyaru yayin da masu kudi ke kara kudancewa, talaka kuma na kara shiga halin ha’ula’i?