Sunday, July 21
Shadow

Ana warkewa daga ciwon zuciya

Ya danganta da irin ciwon zuciyar daya kamaku, mun yi bayani akan kalolin ciwon zuciya da ake dasu, Alamomin ciwon zuciya

Idan ciwon zuciyar Coronary artery disease ne ya kamaka, maganar gaskiya ta masana kiwon lafiya sun ce ba’a warkewa daga kalar wannan ciwon zuciya.

Yanda zaka san kalar ciwon zuciyar da ya kamaka shine ka yi magana da likitanka ko kuma ka karanta takardar sakamakon gwajin da aka maka.

Da zarar likitoci sun tabbatar da cewa wannan kalar ciwon zuciyar ne kake dashi to bai da magani, saidai akwai hanyoyin da ake bi dan kada wasu sauran matsaloli irinsu bugun zuciyar farat daya ya kama mutum.

Karanta Wannan  Maganin bugawar zuciya da sauri

Masana sun ce idan irin wannan ciwon zuciya ya kamaka, yana da kyau ka rika kula da cin abinci me gina jiki, ba komai zaka rika ci ba.

Motsa jiki akai-akai shima yana taimakawa masu irin wannan ciwon zuciya sosai.

Hakanan rage shan giya ko kumama daina shanta kwata-kwata yana taimakawa matuka ga me irin wannan ciwon zuciya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *