fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Ana zargin bam ya tashi a mashaya a Jihar Kogi

Rahotanni daga garin Kabba da ke Karamar Hukumar Kabbah-Bunu a Jihar Kogi ta arewa maso tsakiyar Najeriya na cewa wani abu da ake zargi bam ne ya fashe a wata mashaya.

Sai dai bayanan farko-farko kan lamarin da ya faru da misalin karfe tara da minti 15 na dare ranar Lahadi, na nuna cewa ba mutumin da ya rasa ransa a fashewar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP William Ovye-Aya wanda ya tabbatar wa da BBC fashewar, ya ce ba su kai ga tantance ainahin abin da ya fashe ba.

Ya ce lamarin wanda ya faru a wata mashaya ta Omofemi a unguwar Okepadi, da ke garin na Kabba, ya yi sanadiyyar lalacewar gini da kujeru da kuma tebura a wurin.

Wannan ba shi ne karon farko ba da ake samun fashewa a wuraren shan barasa a garin na Kaba, inda ko a ranar 11 ga watan Mayu na 2022, wani bam ya tashi a yayin da ake bushasha a wani gidan giya a garin.

Fashewar wadda ta auku da misalin karfe goma saura kwata na dare a wancan lokacin, rahotanni sun ce ta yi sanadiyar mutuwar mutum akalla uku, tare da jikkata wasu da yawa.

Ana samun irin wannan fashewa a wuraren shan barasa da dama a arewacin Najeriya, inda a baya-bayan ta auku a jihohin Yobe da Kaduna.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.