Monday, March 30
Shadow

Ana Zargin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari, Na Dauke Da Cutar Corona Virus

Abba Kyari, Shugaban Ma’aikatan fadar Shugaban kasa, ya ce ba shi da lafiya sosai kuma a zahiri ana zargin ya kamu da cutar Coronavirus, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

 

 

Wata majiyar gwamnati ta fada wa Sahara Reporters a ranar Litinin cewa Kyari ya yi matukar jinya, tun bayan dawowar shi daga kasar waje.”

 

 

Kyari ya ziyarci Jamus da Misira ne kawai ya dawo a wannan makon, inda ya ba da tabbaci game da gaskiyar cewa watakila ya kamu da cutar.

 

 

Kasar Masar tana da adadin 327 da aka tabbatar sun kamu da cutar Coronavirus da kuma 14 da suka mutu yayin da Jamus ke da mutum cutar 29,056 da suke dauke da cutar, 123 kuma sun mutu.

 

 

Duk da cewa ya na fama da cutar tari sosai, an ce yana halartar tarurruka tare da Buhari, da Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo, da ministoci da sauran membobin Majalisar zartarwa ta tarayya.

 

 

Shugaban zartarwa na Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya, Farfesa James Momoh, ya ce ya raka Kyari a yayin ziyarar kasashen biyu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *