fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Anawa Fulani Musulmai kisan mummuke a Kudancin Kaduna>>Kungiyar kare muradu musulmai ta MURIC ta koka

Kungiyar kare muradun musulmai ta MURIC ta koka da cewa matasan Kiristoci A Zangon Kataf a kudancin Kaduna nawa Fulani Musulmai kisan mummuke.

 

Shugaban kungiyar,Ishaq akintola ne ya bayyana haka a sanarwar daya fitar yau, Litinin inda yace an kaiwa Fulani sabbin hare-hare a ranekun 8 da 9 ga watan Satumba duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi.

Yace harin yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 4. Hari na farko ya farune a kusa da Gora Gan inda matasan Kiristocin suka kashe, Abdullahi Hassan, Yusuf Hassan Sogiji da Abubakar hassan hakanan mutane 2, Musa Hassan da Malam Hassan an kaisu Asibitin Jama’a dake Zonkwa bayan samun raunuka yayin harin.

 

Karanta wannan  Bincike ya nuna cewa rabin 'yan Najeriya zasu fada talauci a karshen shekarar 2022

MURIC ta kuma bayyana cewa hafi na 2 ya farune ranar Laraba,  9 ga watan Augusta a Kurmin Masara kusa da gadar Bakin Kogi inda Matasan Kiristocin suka kashe Abdulrashid Lawal Malan. Hakanan wani Maitalata Idris Narutu ya tsallake Rijiya da baya bayan da wasu matasan Kiristoci suka tareshi a kan titi.

 

MURIC tace tana Allah wadai da wadannan hare-haren kuma tana kira ga hukumomi da su dauki matakan da suka dace dan kawo karshen su. Ta yi kira da a kai sojoji a ajiye a wajan har sai an samu zaman lafiya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.