fbpx
Saturday, March 25
Shadow

Anga Gwamonin Kaduna da na Ekiti tare a coci, bayan da gwamnan Kadunan ya kunyata na Ekitin a kwanakin baya: Gwamnan Kaduna ya cire hularshi a coci:Hakan ya jawo cece-kuce

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai da shugagabar hukumar kula da tashoshin ruwan najeria, NPA a takaice, watau Hadiza Bala Usman kenan tare da gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose kenan a wannan hoton inda suke zaune a cikin wata coci a cikin jihar Ekitin dan halartar jana’izar mahaifiyar wani sanata data mutu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wannan shiga coci da Gwamnan jihar Kaduna yayi kuma ya cire hularshi , irin yanda kiristoci keyi, ya jawo cece-kuce, wasu dai na ganin hakan da yayi ba daidai bane domin yayi koyi da kiristocin a matsayinshi na musulmi.

Wasu kuma na ganin ai ba komai bane indai ya tsarkake zuciyarshi kuma bai rika fadar amin ba a cikin addu’o’in da za’a rika yi a cikin cocin ba.
Wani da yayi sharhi akan wannan hoton har kalaman da basu kamata ba ya gayawa gwamnan(zagi) inda da yawa akayi caa!! Akanshi aka gayamishi ba daidaibane zagin shuwagabnni.
Haka kuma wani abu daya kara jan hankulan mutane akan wannan hoto shine irin yanda gwamnonin biyu ke da mabanbantan jam’iyyoyin siyasa da kuma ra’ayin siyasa amma aka gansu suna zaune a guri daya har suna raha.
Hakan yasa wasu suka rika jawo hankulan masu ra’ayin siyasar gani kasheni dasu hankalta, domin kuwa mafi yawancin manyannan kansu a hade yake.
Za’a iya tuna yanda gwamnan jihar Ekitin, kwanannan yayi magana akan korar malaman makarantar firaimare na jihar Kaduna inda yace jam’iyyar APC korar ma’aikatane ta saka a gaba, inda ya bayar da misali da jihar ta Kaduna, gwamnan jihar Kadunan, a wancan lokacin ya kunyata Gwamnan Ekiti da irin amsar daya bashi wanda har hakan ya dauki hankulan mutane sosai.
To amma yau gasu a guri daya zaune suna raha, wannan ya ishi masu siyasar gani kasheni akan wani dan siyasa hankali


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Allah Ya Amsa Baba!

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *