fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Ansu Fati ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya bugawa Sifaniya wasa cikin shekaru 84

A yaune kasar Jamus ta bugawa wasa da Sifaniya a gasar cin kofin kasashen Nahiyar Turai. Wasan ya kare da sakamakon kunnen doki 1-1.

 

Tauraron dan wasan Sifaniya, Ansu Fati ne ya dauki hankulan mutane a wasan bayan da ya zama dan wasa mafi karancin shekaru,17 da ya bugawa kasar Sifaniya wasa a cikin shekaru 84 da suka gabata.

Angel Zubieta ne na karshe mafi karancin shekaru da ya bugawa Sifaniya wasa a shekarar 1936. Ansu Fati ya ci kwallo amma aka kasheta saboda wata Keta da Sergio Ramos yayi.

Karanta wannan  Cristiano Ronaldo na son barin Manchester United ne saboda Lionel Messi, karanta kaji dalili

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.