fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Antonio Rudiger ya koma Real Madrid

Real Madrid ta tabbatar da daukar dan wasan bayan Jamus da ya buga kwallo a Chelsea Antonio Rudiger.

Dan bayan Jamus din ya sanya hannu ne kan yarjejeniyar shekara hudu tsakaninsa da Madrid.

Zai koma Bernabeu a matsayin kyauta bayan kin amincewa da ya yi Chelsea ta sabunta kwantaraginsa.

Rdiger ya zabi komawa Madrid maimakon kungiyoyi irinsu PSG da Juventus da kuma Manchester United.

Kungiyar ta ce za ta gabatar da shi ne a filin wasanta gaban magoya baya a ranar 20 ga watan Yuni.

Leave a Reply

Your email address will not be published.