Anya Badakar Aisha Buhari Da Aminu Ba Za Ta Shafi Takarar Tinubu A Yankuna Arewa Ba?
Daga Ishaqah Sa’idu Gambo
Ni kam Tinubu nake tausaya a badakalar Aisha Buhari da Aminu Dan Makaranta, domin yin shirun sa kan lamarin ka iya jawowa takarar sa matsala a matsayin ta na shugabar masu yakin neman zaben sa a bangaren mata.
Duba da irin wannan abu da ya faru tsakaninta da Aminu, ba na tunanin yawon yakin neman zaben Tinubu da za ta jagoranta ya yi tasiri a yankunan Arewa.
Ko dai da biyu ta yi hakan ne don kada Tinubu ya ci zabe?