fbpx
Sunday, December 4
Shadow

Anyi Allah wadai da shafin Sahara Reporters bayan da suka wallafa labarin Allah kara ga ciwon kafa daya hana IBB saka takalmi

Shafin kwarmato labarai na Sahara Reporter ya wallafa wani labari akan tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida, IBB da jama’a basu ji dadinshiba kuma akata Allah wadai da hakan, shafin dai ya bayar da labarin cewa wai Allah ya kama IBB din, tun bayan daya soke zaben Abiola na june 12.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Kamar yanda Saharar ta wallafa tace, tun bayan soke zaben na Abiola da IBB din yayi wai sai aka samu wasu musulmai suka a jiharshi ta Naija suka sace takalminshi a lokacin daya shiga masallaci yin sallah, wai tun daga nan (shaidanin)IBB din, kamar yanda suka kirashi, baya iya saka takalmi har zuwa yanzu.
Bayan wallafa wannan labari, mutane mafi rinjaye da suka bayyana ra’ayoyinsu akai sunyi Alah wadai daahi, da yawa sunce ai cuta ta Allahce kuma babu wanda yafi karfin ta sameshi, Kuma irin salon da Sahara Reporters din suka bayar da labarin ya nuna cewa suna jin dadin halin da IBB din yake ciki, wanda hakan bai daceba.
Wasu dai har sun fara kira da cewa shafin na Sahara ya cire wannan labari dan bai daceba, wasuma sunce karyane, ciwone IBB din yaji shiyasa baya iya saka takalmi, bawai sihiri aka mishiba.
Ga kadan daga cikin abubuwan da da wasu suka ce akan wannan labari:


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Anya kuwa da gaske gwamnati tana so ta kasheni>>Bello Turji

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *