A yau Alhamisne aka binne gawar matar tsohon gwamnan Jihar Gomne Hajiya Yalwa Danjuma Goje a garin Gombe, dubun-dubatar mutanene suka halarci jana’izar Hajiya Yalwa haka kuma manyan jami’an gwamnati da suka hada da kakakin majalisar dattijai Bukola Saraki da ministan ilimi Malam Adamu Adamu da sauransu.
Hajiya Yalwa ta rasu a kasar Amurka inda taje yin jinya ranar 30 ga watan Octoba .
Muna fatan Allah ya jikanta in tamu tazo yasa mu cika da Imani