Shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu ya bayyana cewa sune zasu lashe zaben shekarar 2023 idan har ba ayi magudi ba.
Adamu ya bayyana hakan ne bayan daya karbi bakucin ambasadan kasar Porland, Joanna Tarnawska a ofishinsa.
Inda yace mata sama da mutane miliyan 43 na son APC saboda haka sune zasuyi nasara, kuma yace mata har mace aka samu a jam’iyyar data tsaya takarar gwamna.
Joanna Tarnawska ta taya Abdullahi Adamu murnar zama shugaban jam’iyyar ta APC kuma ta koka aka matsalar tsaron da Najeriya ke fama dashi, inda tace kasarta ta taba shiga cikin wannan halin.