fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

“APC ka iya fadi zaben shekarar 2023 idan har shugaba Buhari ya tsayar da dan takara”>>Membobin jam’iyyar

Membobin APC da dama sun kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari akan ra’ayinsa na zabar dan takarar da zai maye gurbinsa a zaben shekarar 2023.

Muhammadu Buhari ya bayyana ra’ayin nasa ne a ranar talata a taron daya yi da gwamoni, kuma wata kungiyar masu hannun jari a jam’iyyar ta bayyana cewa hakan ka iya sa APC ta fadi zaben shekarar 2023.

Inda shugaban kungiyar Aliyu Audu ya bayyana cewa mafi yawancin abinda kesa dan siyasa yayi nasara shine ta yadda aka tsayar da shi a matsayin dan takara, ba wai sanin ko waye shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.