Rahotanni sun bayyana cewa, jam’iyyar APC ta dauko hanyar lalacewa yayin da da yawa daga cikin jam’iyyar suka bayyana cewa, basu yadda da tsarin shugaban kasa na samar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ba tare da yin zabeba.
Hakan na faruwa ne yayin da wasu majiyoyi ke cewa shugaban kasar ya zabi mataimakinsa, Farfeaa Yemi Osinbajo a matsayin wamda yake son ya gajeshi.
Saidai wasu hadda masu yiwa shugaba Buhari biyayya sosai irin su gwamnan Kogi, Yahya Bello na cewa shugaban kasar yasan abinda zai yi ya hada kan jam’iyyar ba tare da ta tarwatse ba.
Tuni dai wasu gwamnonin jam’iyyar suka fara ganawa a Abuja dan samar da dan takarar kamar yanda shugaban kasar ya bukata.
Wata majiya daga wajan tarin da gwamnonin ke yi ta shaidawa jaridar Vanguard cewa, nan da kamin karshen mako gwamnonin zasu samu matsaya akan wanda za’a tsayar yawa jam’iyyar takarar shugaban kasa.
Hakanan kuma majiyar tace duk wanda ya yadda ya janye za’a mayar masa da Miliyan 100 ta sayen fom ko kuma a bashi mukami a sabuwar gwamnatin da za’a kafa idan APC ta ci zabe.