fbpx
Monday, March 1
Shadow

APC ta kara wa’adin makwanni uku domin cigaba da rijistar Jam’iyyar

Jam’iyyar (APC) ta ce biyo bayan kiraye-kirayen da ake yi na tsawaita rijistar mambobin Jam’iyyar a fadin kasar jam’iyyar taga da cewar kara wa’adin aikin har na tsawan makwanni uku.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataran jam’iyyar na Kasa Sanata John Akpanudoedehe ya fitar, inda ya bayyana farin ciki kan gagarumar nasarar da aka samu a aikin musamman a jihohin da ke karkashin ikon jam’iyyar adawa.

Idan zaku tuna, Jam’iyyar APC mai mulki ta fara yin rajistar mambobin ta tare da sabunta katin jam’iyyar ga tsoffin cikin ta a ranar Talata 9 ga watan Fabrairu, 2021 a duk fadin jihohi 36 na tarayyar kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *