A jiya ne jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sake sanya ranar sayar da fom din tsayawa takarar mukamai zuwa wani mako wanda tun farko ta sanya a yau.
Sabbin shugabannin jam’iyyar sun kuma tura dukkan daraktocin jam’iyyar 6 a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa da ke Abuja hutun dole.
Jaridar The Nation tattaro cewa an sanar da sake jadawalin siyar da fom ne sakamakon gazawar ɗan kwangilar da ke kula da buga fom ɗin akan lokaci.