Jam’iyyar mai ci ta APC ta taya ‘yan uwa musulmai na fadin kasar Najeriya dama duniya bakidaya murar shiga sabuwar shekara.
Inda kuma ta bukacesu dasu cigaba da baiwa shugaba Muhammadu Buhari goyon baya dari bisa dari.
Yayin da kuma tace su cigaba da yiwa kasara addu’ar shawo kan matsalar tsaro da kuma zaman lafiya mai dorewa.