fbpx
Monday, August 15
Shadow

APC tace fadi zaben jihar Osun ba shi zai hana Tinubu lashe zaben shugaban kasa ba a shekara mai zuwa

Shugaban jam’iyyar mulki ta APC dake jihar legas, Abayomi Mumuni ya bayyana cewa fadi zaben gwamnan jihar Osun da jam’iyyar tayi ba zai hana Tinubu lashe zaben shugaban kasa ba.

Abayomi Mumuni ya bayyana hakan ne a yau inda yace jam’iyyar ta dauki darasi bayan ta fadi zabenta da PDP saboda haka ba zata maimaita ba.

Kuma a karshe tsohon dan takarar gwamnan jihar Legas din yace baiji dadin fadin zaben da sukayi ba amma duk da haka ba zai hana su cin zabe a shekara mai zuwa ba.

Karanta wannan  Ba zan tana bari kungiyar malamai ta tafi yajin aiki a mulkina ba, cewar Atiku Abubakar

A ranar lahadi ne hukumar zabe ta INEC ta bayyana cewa dan takarar PDP Ademola Adeleke ne yayi nasarar lashe zaben gwamnan jihar Osun.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.