fbpx
Monday, June 27
Shadow

Arewa, Zaben 2023, Atiku Da Kwankwaso

Daga Datti Assalafiy

Tambihi da Tunatawar:
Ya kamata duk wani ‘dan Arewa ya tuna da cewa: Tun bayan dawowar Nigeria kan tsarin mulkin Demokaradiyyah a 1999, Obasanjo yayi shekaru 8 yana mulki, Jonathan yayi shekaru 6 yana mulki, idan an hada lissafi Kudancin Nigeria sunyi shekaru 14 suna mulki

Idan an dawo Arewa, ‘Yar-adua yayi shekaru 2 yana mulki Allah Ya karbi rayuwarsa, shugaba Buhari zaiyi shekaru 8 yana mulki, idan an hada lissafi, Arewacin Nigeria sunyi shekaru 10 suna mulkin Nigeria a tsarin Demokaradiyya.

Don haka a babin adalci, idan ma batun karba-karba ake tsakanin kudanci da Arewacin Nigeria, har yanzu Arewa tana da sauran wa’adin mulki daya da ya rage wato shekaru 4 idan Buhari ya kammala, don haka dole ayi adalci a bar mulki a Arewa.

Makasudin Rubutu:
A zaben 2023 mai karatowa, muna da manyan ‘yan siyasa guda biyu da suka fito takaran shugaban kasa a Arewa, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP daga yankin Arewa maso gabas, sai kuma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP daga yankin Arewa maso yamma.

Atiku Abubakar da Kwankwaso suna da dunbin mabiya a Arewacin Nigeria, don haka tsayawarsu takaran Shugaban Kasa a lokaci guda mummunan harin bomb ne da zai iya tarwatsa kuri’un ‘yan Arewa a zaben 2023 a wayi gari kudancin Nigeria sun samu mulki cikin sauki.

Atiku Abubakar idan bai fi Kwankwaso yawan mabiya ba a Arewa to zasuyi kunnen doki, to amma idan aka duba dayan bangare, Atiku Abubakar yafi Kwankwaso yawan mabiya a bangaren kudancin Nigeria nesa ba kusa ba, Kwankwaso yawan mabiyansa da farin jininsa a Arewa ne musamman jihar Kano.

Sannan mu duba da kyau, Gwamnoni nawa Kwankwaso yake da su a NNPP?, ina tsamman babu ko guda daya, wani Gwamna ne zai iya kawo masa jiha? amsa shine babu.

Amma PDP fa? akwai Gwamnoni masu ci da taoffin Gwamnoni a PDP, akwai manyan ‘yan siyasa har ma da tsoffin shugabannin Kasa a PDP, don haka PDP ta fi NNPP karfi da samun damar kwace mulki daga APC a zaben da za’ayi.

Duk wanda ya san Nigeria, kuma yana yawo a sassan Nigeria, yana la’akari da dabi’un da halayyar mutanen Arewaci da Kudancin Nigeria akan rayuwarsu da siyasa, ya san cewa Kwankwaso ba zai iya kawo Nigeria ba indai zabe za’a yi, Atiku Abubakar ne yake da wannan tasirin, domin duk wani ‘dan siyasa da yake son ya kawo Nigeria dole sai ya samu kuri’a daga kudanci da Arewacin Nigeria.

Karanta wannan  Tinubu ya sasanta da sanatocin APC sun fasa sauya sheka, cewar Kashim Shettima

Kwankwaso jagoran talakawa ne, yawanci talakawa ne sarakunan yakinsa a Siyasa, jam’iyyar NNPP da ya koma bata da wani karfi da tasiri, babu wasu manya da suke tare da jam’iyyar, Kwankwaso bai da kayan aiki da zai iya baje hajarsa a kudancin Nigeria, a Arewacin Nigerian ma ba ko’ina ba imbanda Kano, Kuma ba yawan masoyan ba, shin suna da katin zabe?, duk wannan gaskiya ne da ya kamata mu fadawa kanmu idan muna kishin Arewa da gaske.

An samu matsala tun daga lokacin da Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar PDP, ban sani ba ko kuskuren fahimta nayi, amma yafi dacewa ace Kwankwaso bai canza sheka ba ya tabbata a jam’iyyar PDP domin ya taimaki Atiku su kwace mulki daga hannun APC saboda Arewa ta cigaba da mulki, tunda Gwamnonin APC sun sha alwashin mulki sai ya koma Kudancin Nigeria.

Ni a ra’ayi na, a samu manyan Malamai da Manyan Sarakuna da Dattawa su daidaita tsakanin Atiku da Kwankwaso, idan an kafa Gwamnati a yiwa Kwankwaso Babban mukami na Minista ya kula da bangaren bukatun talakawa.

Amma matukar Kwankwaso zai yi takaran shugaban Kasa, Atiku ma zaiyi takara to ba shakka mulki zai iya kubucewa daga Arewa, haduwarsu yafi alheri akan rabuwar, sannan Kwankwaso ya marawa Atiku baya shine abinda yafi dacewa.

Kwankwaso nagartaccen shugaba ne da ya kamata a cigaba da tafiya dashi ko don amfanar talakawa, bai kamata a kafa Gwamnatin da babu Kwankwaso a cikinta ba, talakawa ne da asara.

Namu hasashe ne da lissafi, amma Allah (T) shine mafi sani akan komai.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya mana zabi mafi alheri.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.