Robert Lewandowski da Thomas Mueller sun yi nasarar zirawa Bayern Muncih kwallye hudu yayin data lallasa kungiyar Arminia 4-1 a gasar Bundlesliga wanda hakan yasa yasa ta koma ta biyu a saman teburin gasar bayan Hoffenhiem ta lallasa su a watan daya gabata.

Kungiyar Bayern Munich, wadda tayi nasarar lashe kofuna uku a kakar data gabata ta fara jagorantar wasan ne ta hannun Mueller a minti na 8 kafin Lewandowski ya zirwa nashi kwallayen guda biyu. Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci shima Mueller ya kara zira wata kwallon kafin a baiwa dan wasan su Tolisso jan kati.
Itama kungiyar Dortmund tayi nasarar cin kwallo guda a wasan tada Hoffenhiem wanda hakan ya kasance karo na farko data ci Hoffenheim a gidan ta cikin shekaru 8 da suka gabata, kuma yanzu makin ta ya kasance daidai dana Bayern Munich a teburin gasar Bundlesliga.
Dortmund ta ajiye Haalanda a benci domin ya huta bayan ya bugawa kasar sa Norway wasanni uku a cikin makonni biyu, amma shigowar sa tare da Reus tasa kungiyar tayi nasarar cin kwallo guda ta hannun Reus a minti na 76.