fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Arsenal na shirin sayen Gabriel Jesus nan da mako guda

Kungiyar Arsenal na shrin sayen dan wasa gana na farko a bana, inda zata dakko Gabriel Jesus daga kungiyar hamayya ta Manchester City.

Arsenal zata saye shi ne a farashin yuro miliyan 50 nan da mako guda, kuma shima dan wasan na son barin City domin ya samu damar buga wasanni sosai.

Bugu da kari Jesus na son barin Manchester ne don ya samu matsugunni a tawagar kasar Brazil da zasu buga mata gasar kofin Duniya na wannan shekarar.

Kuma akwai wasu manyan kungiyoyin dake son sayen dan wasan kamar Real Madrid, Tottenham da Chelsea, amma da diyiyuwar tsohon kocinsa Arteta na Arsenal me zai yi nasarar sayen shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.