fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Arsenal ta yi kane-kane a mataki na hudu a teburin Premier League

Arsenal ta jaddada matsayinta na shiga gasar Zakarun Turai ta Champions League a kakar badi.

Gunners din ta yi nasarar doke Leeds United da ci 2-1 a wasan mako na 36 da suka fafata a Emirates ranar Lahadi.

Eddie Nketiah ne ya fara ci wa Gunners kwallo minti biyar da fara wasa, sannan minti biyar tsakani ya kara na biyu.

Leeds United ta farke daya ta hannun Diego Llorente, amma ta karasa karawar da ‘yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Luke Ayling jan kati tun a minti na 27 da fara tamaula.

Karanta wannan  Malamin Sakandiri ya zane dalibinsa har ya fara amai a karshe ya mutu saboda bai kammala Home-Work ba a Legas

Da wannan sakamakon Arsenal ta ci gaba da zama a mataki na hudu a teburin Premier League da maki 66 da tazarar maki hudu tsakaninta da Tottenham, wadda ke mataki biyar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.