fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Arsene Wenger: Tsohon manajan Arsenal ya bayyana dan wasan da zai maye gurbin Cristiano da Messi

Tauraron Juventus Cristiano Ronaldo da zakaran Barcelona Lionel Messi sun mamaye duniyar wasan kwallon kafa kuma ya sun lashe kyautar balloon d’Or har sau 11 a shekaru 12 da suka gabata kuma masoyan wasan kwallon kafa basu taba ganin jaruman da suka samu irin nasarorin da suka samu ba.

Tsohon manajan Arsenal Arsene Wenger yace Mbappe shine zai maye gurbin Cristiano Ronaldo da Lionel Messi. Wenger ya gayawa manema Labarai na Talk Sport cewa ba’a taba samun yan wasa kamar Ronaldo da Messi ba a duniyar wasan kwallon kafa amma yanzu sun kusa yin ritaya kuma Mbappe ne zai maye gurbin su.
Dan wasan faransan shine ya zo na shida a kyautar balloon d’Or na shekarar bara yayin daya biyo bayan yan wasan Liverpool guda uku Virgil Van Dijk da Sadio Mane da Mohammed Salah.
Wenger yace ba wai yana cire Neymar bane a cikin jerin sunayen yan wasan da zasu maye gurbin Ronaldo da Messi ba.
Mbappe yaci kwallaye guda 90 a wasanni guda 120 daya buga a kungiyar PSG kuma ya lashe gasar kofin duniya a shekara ta 2018 abun da Messi da Ronaldo basu taba yi ba.
Wenger ya kara da cewa suma yan wasan ingila ba’a bar su a baya ba saboda matasa ne kuma suna kokari sosai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.