A jiya ranar juma’ biyar ga watan Augusta aka far buga kakar wasan bana ta gasar Firimiya a kasar Ingila.
Inda aka fara buga wasa na farko tsakanin Arsenal da Crystal Palace, inda Gunners tayi nasarar lallasa Palace daci biyu ta dare saman tebur.
G. Martinell ne ya fara ciwa Arteta kwallo guda kafin daga bisani bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ana daf da tashi wasa M. Guehi yayi kuskuren cin gida.
Inda aka tashi wasan Mikel Arsenal na cin Palace 2-0 kuma ta dare saman tebur, wanda hakan yasa Arteta ya zamo kocinta na biyu daya yi nasarar cin wasanni 50 cikin kankanin lokaci a wasanni 98, bayan Arsene Wenger wanda yaci a wasanni 94.