fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Arzikin Dangote ya ƙaru da dala biliyan biyu

Arzikin Aliko Dangote ya ƙaru matuƙa yayin da yake yunƙurin kammala shekarar 2021 da arzikin da bai taɓa samu ba cikin shekara bakwai sakamakon haɓakar ribarsa a ɓangaren siminti.

Haɓakar kasuwar hannun jari a kamfaninsa na siminti da kuma tashin farashin man fetur da takin zamani sun taimaka wa Dangote inda dukiyarsa ta ƙaru da dala biliyan 2.3 a 2021 zuwa biliyan 20.1 jumilla, kamar yadda mujallar Bloomberg ta ruwaito.

Rabon da dukiyarsa ta kai yawan haka tun 2014, lokacin da ta kai dala biliyan 26.7 a watan Yunin shekarar, a cewar jaridar.

Tashin farashin kayayyakin gini a Najeriya, wadda ke da mafi girman tattalin arziki a Afirka, sun haɓaka ƙarfin jarin kamfanin Dangote Cement plc.

Nan gaba kaɗan ake sa ran Dangote zai kammala ginin matatar man fetur kan dala biliyan 19, wadda za ta dinga samar da fetur fiye da abin da kasuwar Najeriya ke buƙata.

A wannan shekarar ce kuma Dangote ya fara fitar da takin zamani zuwa Amurka da Brazil bayan kammala ginin ma’aikatar taki da ke iya samar da taki tan miliyan uku duk shekara.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.