fbpx
Monday, June 27
Shadow

Ashe Delegates din Kano basu zabi Atiku ba saboda Kwankwaso,Wike suka zaba

Rahoto daga Premium times ta bayyana kan yanda Delegates din da suka yi zabe a zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP suka kada kuri’unsu.

 

Ariku ya samu kuri’u 371 sa Wike ya sami 237. An jefa jimullar kuri’u 767.

 

Jihohin Arewa maso yamma, Kano, Katsina, Jigawa, Zamfara, Kebbi, Sokoto da Kaduna sun je da Delegates 193.

 

Atiku ya lashe gaba dayan jihohi 5 in banda jihar Kano wanda Delegates dinta suka zabi Wike suka bashi gaba dayan kuri’unsu 44.

 

Hakan ba ya rasa nasaba da Kwankwaso wanda tsohoj jigo ne a jam’iyyar PDP ta Kano kuma ana ga kamar basa ga maciji da Atiku.

 

Saidai Delegates din Katsina wasu sun zabi Wike wasu sun zabi Atiku inda aka yi raba daidai.

 

A Arewa ta tsakiya kuwa, Bukola Saraki ya cinye jihrsa ta Kwara, sai kuma a Jihar Naija da aka raba kuri’u tsakanin Atiku da Wike.

 

Atiki ya lashe Filato da kuma mafi yawancin kuri’ar jihar Nasarawa, Wike ne ya lashe babban birnin tarayya, Abuja.

Karanta wannan  Zulum ne kadai Tinubu zai zaba a matsayin abokin takararsa idan har yana so yayi nasara akan Atiku, cewar kungiyar masu hannu da tsaki na jam'iyyar APC

 

Gwamna Udom Emmanuel ya samu kuri’u daga jihar Benue inda Atiku da Wike suka raba sauran kuri’un.

 

In banda Bauchi da suka zabi Gwamna Bala Muhammad da kuma Taraba da aka yi raba daidai tsakanin Wike da Atiku, Atiku ne ya lashw sauran duka jihohin Arewa maso gabas din.

 

Jihohin Kudu maso yamma na Ekiti, Lagos, Ogun, Ondo, Osun da Oyo kuwa sun yiwa Atiku da Wike, da Saraki raba daidai din kuri’unsu.

 

A jihohin kudu maso kudu, Wike ya lashe Cross-Rivers, Edo da Rivers, Delta da Bayelsa kuwa sun zabi Atiku ne sai gwamna Udom Emmanuel da ya lashe Akwa-Ibom.

 

A jihohin Inyamurai kuwa, Wike ya lashe Abia da Enugu Atiku ya cinye Anambra da Imo, sai Pius Anyim ya lashe Ebonyi.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.