fbpx
Friday, August 12
Shadow

Ashirye nake don sasantawa da gwamna Wike, cewar Atiku Abubakar

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa a shirye yake don sasantawa da gwamnan Rivers Wike.

Atiku ya bayyana hakan ne a jihar Osun bayan yaje taya dan takarar gwamnan PDP Ademola Adeleke yakin neman zabe tare da sauran shuwagabannin PDP.

Kuma Atiku ya cewa manema labarai babu wani sansanin Atiku da sansanin Wike, PDP jam’iyya guda ce sansani guda suke da shi na kowa da kowa.

Kuma a shirye yake ya sasanta da gwamna Wike wanda ya fusata saboda bai zabe shi a matsayin abokin takararsa ba na zaben shekarar 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published.