Ofishin jakadancin kasar Amurka dake Najeriya ya bayyanawa ‘yan kasar Amurkar dake son komawa gida cewa sune fa zasu biya kudin jirgin nasu.
Sanarwar da ofishin ya fitar ta kara da cewa, kuma jirgin da zai daukesu daga Najeriya a guri daya zai ajiye, kuma kowa shi zai kai kanshi gida, babu tallafin kosisi.
Sanarwar ta gargadi ‘yan Amurkar cewa su sani matsalar Coronavirus/COVID-19 ta sha kan tsarin lafiyar Kasar inda a yanzu asibitocinsu makil suke da mutane.
Sannan su sani a yanzu an dakatar da insorar lafiya,idan zaa dubasu to kowa zai biya kudin dubashine daga cikin aljihunsa.
Sanarwar ta kara da cewa kuma da yawa daga cikin Otal-otal na kasar sun kulle ko kuma suna shirin kullewa, dan haka duk wanda zai koma gida ya tabbatar ya tanadi gurin zama.
Sanarwar ta kara da cewa,Najeriya ta kulle iyakokinta da tashoshin jiragen samanta yanda babu jirgin kasuwa dake sauka a kasar daga kasar waje.
Ta kara da cewa dan haka duk wanda ya bar Najeriya Gwamnatin kasar ta Amurka ba zata taimaka masa wajan dawowa Najeriya ba, saidai ya jira har lokacin da aka bude filayen jiragen kasar, ya bi na haya ya dawo.
Sanarwar ta kara da cewa wannan bayani ya zama dole lura da cewa ya kamata awa ‘yan kasar ta Amurka bayanin halin da gida ke ciki.
Akwai dai mutane 336,851 da suka kamu da Coronavirus/COVID-19 a Kasar Amurka inda mutane 9, 620 suka mutu 17,977 kuma suka warke.