fbpx
Friday, August 12
Shadow

ASUU ta mayarwa da shugaba Buhari martani kan maganar daya yi na cewa su gaggauta janye yajin aiki yara su koma makaranta

Kungiyar malaman jami’ar Najeriya ta ASUU ta mayarwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari martani kan maganar daya yi na cewa yajin aikin nasu ya isa haka nan.

Buhari ya bayyana hakan ne a wasikar data fito daga hannun hadiminsa Garba Shehu, inda yace su bar dalibai su koma makaranta.

Shugaban kungiyar ASUU, farfesa Emmanuel Osodoke ne ya bayyanawa manema labarai cewa basu san abinda Buhari yake nufi da cewa yajin aikin nasu ya isa ba.

Inda yace sun kammala tattaunawa da gwamnatin akan maganar tace zata neme su amma har yanzu shiru.

Leave a Reply

Your email address will not be published.