Kungiyar dake yiwa dan takarar shugaban kasa na APC Asiwaju Bola Ahmad Tinubu Kamfe tace Atiku babban makaryaci ne.
Mungiyar ta bayyana hakan ne bayan Atiku ya caccaki Tinubu yayin daya ke ganawa da Arise TV ranar juma’a.
Inda yace bai kamata Tinubu ya tsayar da Musulmi a matsayin abokin takararsa ba shima yana Musulmi, hakan ba daidai bane kuma dama shi akidar shice hakan ta shigoda addini cikin siyasa.
Wanda hakan yasa kungiyar dake yiwa Tinubu kamfe ta soki Atiku tace karya yake yiwa Tinubu duk abinda ya zayyajana jiya ranar juma’a.