fbpx
Monday, August 15
Shadow

Atiku Abubakar, Okowa da Davido sun mamaye jihar Osun domin taya Adeleke yakin neman zabe

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da abokin takararsa Ifeanyi Okowa sun ziyarci jihar Osun don taya Adeleke yakin neman zabe.

Ademola Adeleke ya kasance dan takarar PDP dake neman gwamnan jihar Osun na zaben da za a gudanar nan da ranar asabar mai zuwa.

Kuma wasu jiga jigan PDP kamar su Bukola Saraki, gwamna Aminu Tambuwa da gwamna Obaseki da fitaccen mawaki Davido duk sun hallaci taron.

Yayin da PDP ta cewa al’ummar jihar kar su zabi APC domin jihar na cikin duhu yanzu a mulkinta, su zabi PDP ta kawo masu agajin gagawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.