
A wata sanarwa da ya fitar ta shafinshi na yanar Gizo watau Atiku.org, tsohon mataimkin shugaban kasa kuma wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa yayi watsi da jam’iyar APC, zaiyi tunanin wace jam’iyya zai koma dan cigaba da harkar siyasarshi.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Wasu daga cikin dalilan daya bayyana da suka tunzurashi barin jam’iyyar sun hada da rashin adalci da kuma rashin bin kudin tsarin jam’iyya da ba’ayi da kuma rashin matasa a cikin manya ma’aikata na kusa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, irin su ministoci da manyan sakatori.
Atiku ya bayyna cewa muddin anaso a kawo cigaba a kasa to dolene fa sai anyi tafiya tare da matasa, ama gwamnatin APC tayiki basu dama.
Atikun ya bayyana irin yanda ‘yan APC din sukaje har gida suka rokeshi akan ya koma jam’iyyar lokacin da yayi watsi da tsohuwar jam’iyyarshi ta PDP saboda rashin adalci da kuma rashin bin kundin tsarin jam’iyya da ba’ayi amma yanzu Atikun yace abinda ke faruwa a jam’iyyar ta APC har yafi na jam’iyyar PDP da ya bari Muni.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Saboda haka shawarar da yayi da iyalai da abokai da ‘yan uwa da kuma zabi da ya baiwa Allah, ya fita daga jam’iyyar ta APC zai zauna yayi nazarin jam’iyyar da ya kamata ya koma.
Saidai kafar watsa labarai ta Daily Trust ta ruwaito cewa tsohuwar jam’iyyarshi ta PDP Atikun zai koma, harma ta bayyana cewa gobene Atikun zai amshi katin jam’iyyar na PDP, kamar yanda wata majiya me karfi ta bayyana mata.
To zamu jira mu gani. lokaci zai bayyana ainihin abinda zai faru.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});