fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Atiku Abubakar ya kaddamar da sabuwar kungiyar matasan Najeriya don cigaba da fafutukar yakin neman zabe

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kaddamar da sabuwar kungiyarsa ta matasa don cigaba da yakin neman zabe.

Atiku Abubakar ya kaddamar da wannan kungiyar ne a babban dakin tarona Shehu Musa Yar Adua dake babban birnin tarayya Abuja ranar asabar.

Inda ya bayyana cewa yana kira ga al’ummar Najeriya dasu ceto wannan kasar daga halin ta take ciki ta hanyar zabarsu a zaben shekarar 2023.

Yayin da shima abokin takararsa Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa an kafa kungiyar don cigaba da fafutukar yakin neman zabe kuma yana fatan al’ummar Najeriya zasu marawa uban gidan nasa baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.