Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya koma jam’iyyar adawa ta PDP. Dan siyasar ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Facebook ranar Lahadi.
Sai dai bai fito fili ya bayyana anniyarsa ta sake neman shugabancin kasar ba yayin sanarwar.
Ya ce ya koma jam’iyyar ne saboda matsalolin da suka sa ya fice daga PDP a shekarar 2014 “an warware su yanzu.” Har ila yau ya ce jam’iyyar APC ta “kasa cika alkawurran da ta yi wa al’ummar kasar musamman matasa.”
A cikin watan jiya ne ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki.
A baya dai Atiku Abubakar ya sha sauya jam’iyyun siyasa. Kuma wannan ne karo na biyu da dan siyasar yake koma wa jam’iyyar PDP. Atiku Abubakar ya kasance mataimakin shugaban Najeriya ne tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.
A shekarar 2007 ne ya fara tsakayawa takarar shugabancin Najeriya ne a karkashin jam’iyyar AC. Hakazalika ya sake neman takarar a shekarar 2011, amma bai samu tikitin jam’iyyarsa ta PDP ba.
Atiku Abubakar ya kara neman tsayawa a shekarar 2014, inda a nan ma bai samu tikitin shugabanci ba a karkashin jam’iyyar APC.
bbchausa.