Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya nada Sanata Dino Malaye a da Mr. Daniel Bwala a matsayin masu magana da yawunsa na kamfe.
Dan takarar ya nada su ne gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2023, kuma hadiminsa Tunde Ibe ne ya bayyana hakan.
Wanda yace ya nada Sanatan jihar Kogin, wato Dino Malaye wanda ya kasance tsohon shugaban sanatoci da kuma Mr. Daniel Bwala, wanda shima fitaccen dan siyasa ne a matsayin hadiman masa na kamfe.