fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Atiku na shirin ganawa da Wike dan a yi sulhu

Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar na shirin ganawa da gwamna Wike dan yin sulhu.

 

Kin daukar Wike da Atiku yayi a matsayin mataimakinsa ya jawo cece kuce a jam’iyyar ta PDP inda wanda suke tare da gwamna Wike ke nuna alamar ficewa daga jam’iyyar.

 

Atiku dai ya tafi kasar Amurka kuma ana ganin cewa idan ya dawo zai gana da gwamna Wike dan yin sulhu dashi.

 

Itama dai jam’iyyar ta PDP na kokarin ganin yin dukkan mai yiyuwa da dawo da zaman lafiya da jituwar juna a cikinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.