fbpx
Saturday, June 25
Shadow

Atiku na son hada kai da Kwankwaso da Peter Obi dan su kwace mulki daga hannun APC

Rahotanni na cewa, dan takarar jam’iyyar PDP na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar na shirin hada kai da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi.

 

Atiku na son yin hadin kanne dan su yaki jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa da zai iya kaisu ga nasara.

 

Duka Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso tsaffin ‘yan jam’iyyar PDP ne kamin daga baya su fice daga cikin ta dan cikar burinsu na zama ‘yan takarar shugaban kasa.

Karanta wannan  Kanzan kurege ne cewa mun bude wuraren rigistar katin zabe a jamhuriyar Nijar, cewar INEC

 

Saidai jam’iyyar PDP na shirin hada kan wadannan ‘yan takarar dan ganin sun tunkari Bola Ahmad Tinubu da gaske.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.