Jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta ce tana jin tausayin tsohon gwamnan Jihar Lagos Bola Tinubu wanda APC ta tsayar takarar shugaban kasa a zaben 2023.
A wata sanarwa da PDP ta wallafa a shafinta na Tuwita bayan an bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani na shugaban kasa a APC, ta ce abin takaici ne yadda ya samu tikitin takara a jam’iyyar da ba ta tsinana wa ‘yan kasar komai ba.
“Jam’iyyarmu tana kuma tausaya wa Asiwaju bisa bin hanyar da ba za ta bille ba domin kuwa shi ba sa’an dan takarar PDP Atiku Abubakar, wanda ya fi kwarewa da kuma shiryawa wajen zaman shugaban kasa; mai hada kai wanda shi ne zabin jama’a,” in ji PDP.
PDP ta siyasar Najeriya ba irin ta Jihar Lagos ba ce inda ta yi zargin cewa Bola Tinubu yana amfani da karfi wajen tursasa wa jama’a.