fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Atiku ya jinjinawa ‘yan wasan Najeriya mata bayan sun samu lashe kyautuka takwas cikin kwanaki hudu a gasar wasannin Commonwealth 2022 a Birmingham

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya jinjinawa ‘yan wasan Najeriya mata bayan sunyi nasarar lashe kyautuka a gasar Commonwealth.

‘Yan wasan Najeriyar sunyi nasarar lashe kyautukan ne a cikin kwanaki hudu kacal a gasar ta Commonwealth 2022 da ake yi a Birmingham.

Inda suka samu lambar yabo ta Gold guda uku sai Silver guda da kuma Bronze guda uku.

Wanda hakan yasa Atiku ya jinjina masu kuma yace suma ya kamata a waiwaye su a taimaka masu domin su kara samun kwarin gwiwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.