fbpx
Friday, August 12
Shadow

Atiku ya kama dani don neman sulhuntawa da gwamna Wike, cewar gwamnan jihar Benue

Gwamnan jihar Benue, Samuel Orton ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na PDP, wato Atiku ya kama dashi don neman sasanci da gwamna Wike.

PDP ta rabu kashi biyu a watanni biyu da suka gabata tun bayan da aka gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar wanda Atiku yayi nasarar lashewa.

Sai gwamna Wike yazo na biyu, kuma masu fadi aji na jam’iyyar sun nemi Atiku ya zabi gwamna Wike a matsayin abokin takararsa amma yaki.

Wand hakan yasa Wike ya fusata sosai tun wancan lokacin, amma yanzu Atiku ya far neman sasanci da gwamna Wike inda Ortom yace ya kama dashi don ya shawo masa kan gwamnan jihar Rivers din.

Leave a Reply

Your email address will not be published.